Libiya: Shekara guda bayan ambaliyar ruwa
September 10, 2024Da ma dai 'yan siyasar kasar da ba sa ga maciji da juna, na kokarin ganin an sake gina yankin da ke da matukar mahimmanci ga tattalin arzikin kasar. Mazauna yankin Derna na kasar Libiya na cike da fatan ganin an sake gina yankinsu da ambaliyar ruwa ta shafa, sakamakon katsewar wasu madatsun ruwa guda biyu a yankin. Duk da wannan fata mazauna yankin na jimamin rasa wasu daga cikin iyalansu da kuma wasu da dama da suka yi batan-dabo, a cikin ruwan da ba za su taba iya yi musu jana'iza ba. Dubban mutane ne suka bace sakamakon ambaliyar, yayin da wasu dubban da ke da sauran numfashi suka rasa muhallansu.
Karin Bayani: Adadin wadanda suka mutu a Libiya ya karu
Gadoji da dama sun karye dubban gidaje sun lalace baya ga asarar dukiya mai tarin yawa da aka tafka, a yankin da ke kasancewa cibiyar kasuwancin Magrib. Mohsen al-Sheikh, mai shekaru 54 cikin yanayi na jimami ya bayyana cewa ya rasa danginsa kimanin 103, sakamakon katsewar madatsun ruwan na Derna. Ambaliyar ruwan ta ranar 10 ga watan Satumbar 2023, ta sake jefa kasar da ke fama da rikici cikin wadi na tsaka-mai-wuya da hakan ya kara tsananin bukatar agajin jin-kai da kuma daukin gaggawa na sake gina kasar ta Libya. Injiniya Salem al-Sheikh da ke aikin sake gina birnin na Derna, ya ce sun cimma kaso mai yawa na sake gina yankin.
Ofishin Kula da Jin-kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce mutane sama da 4,000 ne suka mutu sakamakon katsewar madatsun ruwan guda biyu a bara, yayin da mutane sama da 9,000 suka bace a cikin ruwa. Kazalika wasu karin mutanen sama da 30,000, sun rasa muhallansu. Galibin mutanen da ke zaune a Derna, na da tsatso da Turkawa da 'yan Spaniya da kuma Larabawa har ma da kananan kabilun da suka fito daga kasashen Arewacin Afrika. Duk da cewa yankin ya fada cikin riciki na ayyukan masu tsattsauran ra'ayi da kuma 'yan kungiyar IS tun bayan guguwar sauyin da ta kifar da gwamnatin marigayi tshon shugaban gwamnatin kama-karyar kasar Mu'ammar Gaddafi a 2011.
Karin Bayani: Libiya: EU da Birtaniya za su kai dauki
Hasashen masana yanayi ya bayyana cewa mahaukaciyar guguwar nan ta Daniel, ita ce ta afku a yankin na Derna da ke kasar ta Libya da ke karkashin ikon dakarun tawaye na gwamnatin Janar Khalifa Haftar da ta ja tunga a yankin Benghazi da kuma ke adawa da hukumomin Tripoli a arewacin kasar karkashin jagorancin Abdul Hamid Dbeibah da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da wasu kasashen yammacin duniya. Masu sanya ido kan ayyukan agajin jin-kai a duniya, sun bukaci hada karfi da karfe wajen sake gina birnin na Derna domin sake tsugunar da al'ummar yankin.