SiyasaAfirka
Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane sama da 60 a Kwango
December 28, 2023Talla
Kimanin mutane 40 ne suka mutu a Gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango, sakamakon ambaliyar ruwa da zaftarewar laka, biyo-bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya, lamarin da ya jefa mutane da dama cikin halin kaka-na-ka-yi.
Karin bayani:Boren adawa da Ruwanda a DR Congo
Kamfanin dillancin labaran na Reuters ya rawaito cewa a birnin Bukavu mutane 20 ne suka mutu, yayin da wasu 20 din suka mutu a Kauyen Burinyi, mai nisan kilomita 50 da Bukavu, bayan saukar ruwan daga Talata zuwa Laraba.
Karin bayani:Kungiyar kasashen Gabashin Afirka EAC ta fara janye dakarunta daga Congo
Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan mutuwar mutane 22 a Lardin Kassai ta Tsakiya, a dalilin zaftarewar kasar bayan ruwan sama, inda mutane da dama suka rasa muhallansu.