Aminu Tambuwal zai tsaya takarar neman shugabancin Najeriya
May 6, 2013An dai dauki tsawon lokaci ana gwagwarmaya, an kuma kaiwa ga dauke hankali na 'yan kasa a cikin rikcin jam'iyar PDP mai mulki rikicin kuma da ya dauki sabon launi tare da tabbatar da takara ta shugaban kasa a bangaren shugaban majalisar wakilan kasar Aminu Waziri Tambuwal, duk da cewar dai bai fito domin tabbatar da bayannin jam'iyar da yake fatan tabbatar da takarar tasa a kai ba.
Mataimakin kakakin majalisar wakilan kasar ya ce lallai ba makawa ga Aminu Wazirin na tsayawa takarar da yanzu haka ta kai ga rabon gari a tsakanin fadar shugaban kasar ta Aso Rock da kuma gwamnonin jihohin kasar da dama.
Tuni dai da ma manya a cikin dattawan kasar kama daga Bola Ahmed Tinubu ya zuwa ga Janar Ibrahim Babangida suka fara kiran ya dace ga shugaban dan shekaru 47 ya fito domin gwada sa'a cikin fagen siyasar kasar mai tsidau da kwalabe a cikin sa.
Fagen siyasar Najeriya ya yi zafi
To sai dai kuma takarar ta Tambuwal na nufin kara yamutsi ga siyasar da yanzu haka ta yi zafi kamar gidan gashin burodi ke kuma neman fuskantar yanayi irin na ko mutuwa ko yin rai.
An dai dama share tsawon kusan shekaru biyu ana zaman fari da tsuma a tsakanin fadar gwamantin kasar da tun da farko ta nuna adawar ta ga bullar ta Tambuwal, domin shugabantar bangaren majalisar dake da tasiri a cikin harkoki na siyasar.
Ana ma dai kallon takarar a matsayin kokari na karin raba kayin PDP a bangaren 'yan adawar kasar da suka share shekaru biyu suna amfani da majalisar ta wakilai a matsayin dandali na adawa a cikin manufofin da gwamantin kasar ke yi wa jagora.
To sai dai kuma a cewar Eng. Buba Galadima dake zaman sakataren jam'iyar CPC mai adawa babu ruwansu balle tsaki a cikin kokarin ta da Musa a cikin gidan Fir'aunan PDP kasar ta Najeriya.
Kwace goruba a hannun kuturu ko kuma siddabarun 'yan adawar tarrayar Najeriya dai tuni dai takarar da daga dukkan alamu ke da goyon bayan 'ya'yan jam'iyar PDP dake cikin majalisar wakilai dai ta fara yin tasiri a cikin dangantakar dake tsakanin fadar shugaban kasar da masu dokar da tuni suka fara ji a cikin jikin su.
Rashin tasirin matakan jan kunne
An dai kwace daukacin aiyukan mazabun da suke yi don samun na fura an maida ga ofishin minista na musamman na shugaban kasar.
Sannan kuma an janye ga batun sakar musu 'yan daunin su na cefane duk dai a cikin kokarin dora su a hanyar jan kunne, a cikin rikicin dake iya kara ruda al'amuran cikin jam'iyar da ta share shekara da shekaru tana nasarar turmushe adawa a cikin gida.
To sai dai kuma a cewar Hon Ahmed Idris dake zaman daya daga cikin 'yan majalisar ta wakilai daga jihar Filato hargagi na gwamantin ba zai sanya su sauya tunaninsu na rana ba ta tsoron tafin hannu ba.
Abun jira a gani dai na zaman tasirin bullar ta Tambuwal dake zaman dan takara na baya baya cikin jerin masu tunanin karfi ya zo a cikin fagen siyasar kasar.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal