1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gyara kan dokokin wucin-gadi a Amirka

February 3, 2021

Shugaban Amirka Joe Biden ya sanya hannu a kan wasu dokokin wucin-gadi guda uku, da nufin warware wasu daga cikin dokokin da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya kakaba.

https://p.dw.com/p/3oq2j
USA Russland | Putin und Biden einig über Abrüstungsvertrag
Sabon shugaban kasar Amirka Joe BidenHoto: Evan Vucci/AP Photo/picture alliance

Shugaban Amirkan Joe Biden ya bayyana dokokin da ya warware din da cewa ba su dace ba, kuma sun janyo wa kasar abin kunya. Jigo a cikin wadannan dokoki ita ce, wadda ta tanadi daukar matakan hada wasu yara su fiye da 600 da har yanzu ake neman iyayensu, bayan da gwamnatin Trump ta raba su a lokacin da suke yunkurin shiga Amirkan ta kan iyakarta da Mexico. Sai kuma wata dokar wadda ta bukaci a yi bitar manufofin tsohuwar gwamnati a kan masu neman mafaka a kasar. Shugaba Biden ya nunar da cewa: "Ina ganin kaso 99 cikin 100 na dokokin wucin-gadi da tsohon Shugaban Amirka ya sanya, ba su da amfani ga tsarin kasarmu, sun saba da al'adarmu a yadda aka san mu, musanman a kan shige da ficen jama'a."

Karin Bayani: Rikicin kasuwanci tsakanin Chaina da Amirka

Biden wanda ya ce tasiri da kasaitar Amirka suna habaka ne a lokacin da take da tsarin shige da ficen jama'a na tsanaki, mai nuna adalci tare da mutunta dan Adam: "Kakana ya taba cewa, falala da Allah Ya yi mana wajen kula da makwabta da hada yara da iyayensu, za su taimaka mu sake mai do da martabarmu, a matsayin kasar da tamkar aljannar duniya ce ga mutane mabukata."

Grenze USA Mexiko | Migranten aus Honduras werden an der Grenze festgenommen
Yara da dama gwamnatin Trump ta raba da iyayensuHoto: John Moore/Getty Images

Shugaban na Amirka wanda a fakaice ya ba da amsa ga masu sukar dokokin wucin-gadin da ya dukufa sanyawa hannu ya ce, ba sababbin dokoki yake bullo wa da su ba, yana kawar da wadanda Trump ya sanya ne da suke nuna halin ba sani ba sabo, kuma suka sabawa sanin ya kamata. Kazalika, ya kuma umarci kwamitin da ya dorawa wannan aiki da ya sake takalo batun ci gaba da hada hannu da kungiyoyi masu zaman kansu a kasashen Amirka ta Tsakiya, domin a ci gaba da ba su agaji.

Karin Bayani: Martani kan kutsen magoya bayan Trump

Koda yake yanzu a hukumance, wadannan dokoki sun bayar da izinin hada iyaye da ‘ya'yan nasu bayan da Shugaba Biden ya sanya hannu a kansu, amma kusan abu ne mayuwaci, duba da cewa an dauki lokaci da raba su, kuma babu wani ingantaccen tsarin bin diddiginsu da aka yi a lokacin da gwamnatin Trump ta raba su. Ana kuma zaton cewa, wasu iyayen za su ji tsoron kawo kansu, domin gudun ka da a damke su a matsayin wadanda suka karya doka. Bincike ya nuna cewa, a zamanin gwamnatin shekaru hudu ta Trump an raba iyalai fiye da dubu biyar da 500, inda daga ciki aka mayar da iyaye fiye da dubu daya da 400 kasashen da suke fito ba tare da 'ya'yansu ba.