Biden: Shugaba mai son aiki da jama'a
January 21, 2021Alokacin da Joe Biden yake yi wa Amirkawa jawabi kan annobar COVID-19, ya rinka maimaita jimaminsa ga wadanda lamarin ya shafa. A kasar Amirka kimanin mutane dubu 400 cutar corona ta hallaka: "Zuciyata na tare da kowanne dan kasa da bisa tilas ya yi bankwana da masoyinsa, sakamakon cutar corona da kuma wadanda ba sa iya magana da abokansu ko ba za su iya gaisawa ba sai ta wayar salula, wanda kuwa ko da jana'izar iyalai da dangi ba sa iya zuwa."
Karin Bayani: Tsarin zababbun wakilai na jihohi
Wannan dai shi ne guda daga cikin abubuwan da ya banbamta sabon shugaban Amirkan Joe Biden da wanda ya gada Donald Trump a kan tausayawa Amirkawa. Inda a lokacin da ya shiga takarar sanata a mazabarsa ta jihar Delaware, duk da cewa kujerar ta jima a hannun 'yan jam'iyyar Republican, Biden ya lashe kujerar da agajin iyalansa duk da cewar yana talaka a wancan lokacin. Makonni kalilan bayan zaben ya gamu da wata masifar da ta sauya rayuwarsa, inda matarsa da dansu daya suka mutu a hatsarin mota suka barshi shi da sauran 'ya'yansa biyu wadanda suma suka samu munanan raunuka.
Biden ya ce zai yi murabus daga kujerar tasa ta sanatan, amma aka ba shi shawarar kada ya yi hakan. An rantsar da Biden a matsayin sanata a cikin asibiti. Kanwarsa mai suna Valerie ta koma gidansa domin kula da 'ya'yansa har sai da ya sake wani auren, shekaru biyar bayan rasuwar iyalin nasa, inda ita ma suka haifi yarin daya. Bayan wasu shekaru, Biden ya sake yunkurin yin murabus daga harkokin siyasa a karo na biyu.
Karin Bayani: Trump ya ce shi yai nasara
A shekara ta 2015, Biden ya zama mataimakin shugaban ksar na wancan lokaci Barack Obama kuma sun yi aiki tare domin samar da inshoran lafiya ga Amirkawa. Sai dai a daidai lokacin da Biden ke kokarin samarwa Amirkawa sauki a fannin kiwon lafiya, sai kwatsam babban dansa Beua ya rasu sakamakon cutar sankarar kwakwalwa.
Biden ya shirya yin takarar shugabancin kasar domin maye gurbin Obama sai dai daga bisani ya yanke shawarar komawa gida domin ksanc ewa cikin iyalinsa. Kwanaki kadan gabanin sauka daga mulki, Obama ya karrama Joe Biden da lambar girmamawa ta zaman lafiya. An kuma shaidi Biden a kan muradunsa na inganta mahalli, kuma a yanzu duniya na matukar jiran ganin matakan da zai dauka a fanni kare mahalli wanda Trump ya yi watsi da shi a zamanin mulkinsa. Haka kuma matamakiyarsa Kamala Harris tana daya daga cikin sanatocin da suka gabatar da kudurin tsarin kare mahalli a Amirka. Don haka a wannan fanni akwai matukar fatan samun sauyi daga Amirka wacce ke kan gaba wajen fitar da hayakin da ke haddasa gurbacewar iska a duniya, wanda kuma ke da matukar illa ga muhalli.