1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta kara daukan matakan yaki da cutar Ebola

October 22, 2014

Ana kara samun taimakon kasashen duniya wajen yaki da cutar Ebola a yankin yammacin Afirka

https://p.dw.com/p/1Da1g
Hoto: AFP/Getty Images/Z. Dosso

Gwamnatin Amirka ta fito da wani tsari na lura da 'yan kasashen da aka samu cutar Ebola na tsawon kwanaki 21 ga duk wanda ya shiga kasar daga cikin kasashen na Gini, da Saliyo da kuma Laberiya. Cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa da bayyana haka, sannan an ware filayen jiragen sama biyar da aka amince 'yan kasashen shiga Amirka ta cikinsu.

Tuni tawogar liktocin da ma'aikatan kiwon lafiya kimanin naasar Kyuba, wadanda za su yi jinya masu cutar Ebola, suka isa Laberiya da Gini.

Jirgin mallakin kasar ta Kyuba ya isa cikin taimakon da kasashen duniya ke bayarwa wajen yaki da cutar Ebola a kasashen yankin yammacin Afirka na Gini, da Laberiya da kuma Saliyo. Kasar ta Kyuba tana cikin kasashen duniya da suka tura likitoci da ma'aikatan lafiya domin tabbatar da dakile cutar Ebola. Kasashen Amirka, da Birtaniya da Faransa gami da Jamus suna ci gaba da tura ma'aikatan lafiya domin tunkarar cutar ta Ebola.

Alkaluman hukumar Lafiya ta Duniya sun nuna cewa fiye da mutane 4500 cutar ta hallaka, yayin da ta kama kusan mutane 10000.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba