Amirka ta zargi Najeriya da take 'yancin addini
December 22, 2019Talla
Sakataren harkokin wajen Amirka Mr Mike Pompeo ya tabbatar da sanya sunan Najeriyar cikin wata sanarwar da ya sanya wa hannu.Hakan ya zo ne daidai lokacin da hukumar kula da kare 'yancin addini ta Amirkar, ta fitar da wani rahoton da ya bayyana Najeriyar daga cikin kasashen.
Wasu kasashen da matakin na Amirka ya shafa sun hada ne da kasar Iran da Pakistan da Rasha da Nikaraguwa da kuma kasar Kuba.Rahoton Amirka ya zargi Najeriya da take hakkin mabiya mazhabar Shi'a; da ma kasancewar wasu bangarorin kasar na bin tsarin Shari'ar addinin Islama.