Amirka za ta hana masu magudin zabe visa
May 16, 2023Gwamnatin Amirka ta dauki wannan matakin hana shiga kasarta ne biyo bayan irin laifuffukan da aka samu mutane da aikatawa a lokacin zabubbukan da aka gudanar a Najeriya a 2023. Wannan ya nuna cewa babu alamu na koyon darasi duk da kokarin amfani da na'urorin zamani don kyautata zaben kasar. Sakataren kula da harkokin kasashen wajen Amirka Anthony Blinken ya ce wannan mataki ne a kan wasu ‘yan Najeriya ba wai a kan kasar ko al'ummarta ba.
'Yan siyasa na Najeriya sun maida martani a kan wannan mataki na gwamnatin Amirka, ciki har da Hon Anas Abdullahi da ke zama dan jam'iyyar APC a jihar Zamfara wanda da shi aka yi zaben na wannan shekara. Dama kungiyoyin farar hula da ke sa ido a zaben Najeriya sun dade suna koke na rashin daukan mataki a kan masu aikata laifuffukan zabe a kasar, abin da ya sanya ci gaba da fuskantar matsala a kasar. Paul James, jami'in da ke kula da sanya idanu a kan zabe a kungiyar fara hula ta Yiaga Africa, ya ce abin ya ishesu.
Sai dai Amirka ba ta bayyana sunayen ‘yan siyasar Najeriya da za ta dauki wannan sabon mataki a kansu ba, har sai kotunan kasar sun tabbatar da sunayensu domin tabbatar da laifin da suka aikata. Ana duba tasirin da wannan zai iya yi don zama darasi ga na baya, kamar yadda Barrister Mainasara Umar, masani a fanin dokokin Najeriya ya bayyana.
Wannan mataki da kasar Amirka ta yi ya nuna cewa ta cika alkawari da ta dauka tun kafin zaben, inda ta ce dukkanin wadanda suka tada hargitsi da yamutsi a lokacin zabe, za ta dauki matakin hana su shiga kasarta.
Tashar DW ta yi kokarin jin ta bakin jami'an gwamnatin Najeriya a kan wannan mataki ba tare da samun nasara ba. Sai dai an dade ana kiran gwamnati da ta nuna cewa da gaske take a fanin kafa kotunan na musamman da za su hukunta masu aikata laifuffukan zabe a kasar.