1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty ta bukaci kare hakkin bil Adama a Najeriya

Kamaluddeen Sani Shawai
May 31, 2019

Najeriya na da dama a karkashin sabuwar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta dakile yadda ake cigaba da take hakkokin bil adama da cin zarafin ‘yan Najeriya.

https://p.dw.com/p/3JZRM
Amnesty international
Hoto: picture-alliance/dpa/W.Kumm

Kungiyar ta Amnety International wacce ta saba fitar da rahotanni lokaci zuwa lokaci a dangane da irin yadda yanayin kare hakkokin bil adama yake kasancewa a Najeriya ta bayyana cewar duba da yadda abubuwa ke gudana a kasar musamman a shekarar 2015 a Zariya na hallaka mabiya ‘yan shi’a 350 da sojoji suka yi da kuma hallaka magoya bayan masu rajin kafa kasar Biafra 150 a tsakanin shekara ta 2015-2016 gami cigaba da cin zarafin ‘yan Najeriya yayin gudanar da zanga-zangar lumana a lokuta daban-daban.

Nigeria Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu BUhariHoto: picture alliance/AP Photo/S. Aghaeze

Kungiyar ta kira da babbar murya ga Shugaba Muhammadu Buhari yayin da ya fara wa’adin mulkinsa na biyu na shekaru hudu ya yi kokarin kawo karshen cin zarafin alumma da take hakkokinsu. Isa Sunusi shine Jami’in yada labaran kungiyar ta Amnaesty a Najeriya.

“Muna bukatar ‘yan Najeriya su fara tambayar ina ‘yancin su yake? domin akasari ba a yin la’akari da shi wajen jawaban shugabannni tare da zayyano batun kare ‘yancin bil adama wannan shine ya sanya muka kaddamar da ajandar kare hakkin bil adama a Najeriya.”

Nigeria Demo für die Freilassung von Ibraheem Zakzaky
Wasu 'yan kungiyar Shi'a a NajeriyaHoto: picture alliance/AP Photo/M. Giginyu

Anata bangare shugabar kungiyar kare hakkokin bil adaman a Najeriya Osai Ojigho tace Amnesty International a shekaru da suka shude ta mayar da hankali a kan batun kisa da gallazawa da haramta fadin albarkacin baki, tsarewa ba bisa doka ba da kame ‘yan jaridu.

“A karkashin wannan jadawalin muna bukatar gwamnatin Najeriya ta duba batun kawo karshe gallagarawar da akewa mata, da kare muradun yara da tabbatar da ganin an share dagwalon yankin Naija Delta da samar da yanayin da masu kare hakkin bil adama za su iya aikin su, da shafe hukuncin kisa.

Kungiyar ta kuma yi nuni da yadda ake cigaba da hallaka mutane a yankin arewa maso gabashin Najeriya a inda wasu suke tsarewa da kuma batun jihar Zamfara a inda ake kashe daruruwan mutane.