Amurka ba za ta yi watsi da Ukraine ba
October 1, 2023A cikin wani jawabi da ya yi ta kafar talabijin shugaba Joe Biden ya jaddada wa abokan adawarsu da al'ummar Amurka cewa al'ummar Ukraine za ta ci gaba da samun goyon bayan Washington. Sannan kuma ya ce ba za su yi watsi da Ukraine ba a cikin mumunan hali da take ciki.
Karin bayani: Amurka da Ukraine na son a yi taron dangi kan Rasha
Wannan furuci na Biden na zuwa ne kwana guda bayan da 'yan majalisar dokokin Amurka suka kada kuri'a domin amincewa ko kin amincewa da tsawaita tallafin da ta ke bai wa Ukraine, inda 'yan majalisar suka dauki matakin tsuke bakin aljihu.
Shugaban Biden ya kuma sha alwashin samar da sabon tsari na ci gaba da samar da kudade ga Ukraine a cikin kwanaki da kuma makonni masu masu zuwa duk da sabanin ra'ayi tsakaninsa da 'yan jam'iyyar Republican.
Karin bayani: Amurka za ta bai wa Ukraine sabon tallafi