Blinken na ziyarar ba zata a Ukraine
September 6, 2023A yayin ziyarar jami'in diflomasiyan na Amurka Antony Blinken, ya yi albishir ga hukumomin Kiev, na ba wa kasar tallafin da ya kai dala biliyan guda domin ci gaba da kare kanta daga dakarun mamaya na Rasha.
Karin bayani: Kawayen Ukraine za su ba ta jiragen yaki
Nan gaba kadan mista Blinken zai gana da shugaba Volodymyr Zelensky da kuma takwaransa Dmytro Kouleba domin yin bitar nasarorin da Kiev ta samu bayan farmakin da ta kaddamar yau da watanni biyu domin karbe iko da wasu yankunan kasar da ke karkashin mamaya.
Karin bayani: Zafafa harin Rasha a Ukraine
Tuni dai Moscow ta yi martani kan ziyarar ta Blinken tana mai zargin Amurka da fakewa da sunan Ukraine domin yin yaki da ita, har ma ta kara da cewa wannan tallafi na Amurka ba zai kawo mata cikas ba kan muradinta a kan Ukraine.