Amurka da China sun amince da mayar da huldar tsaro
November 16, 2023Amurka da China sun amince da mayar da huldar al'amuran da suka shafi tsaro wadda ta yi tsami a baya, bayan kammala wata ganawa ta sa'o'i 4 a tsakanin Shugaba Joe Biden na Amurka da takwaransa na China Xi Jinping jiya Laraba a California, ko da yake an jiyo Mr Biden na cewa har yanzu yana kallon Shugaba Xi a matsayin dan kama-karya.
Karin bayani:Barazanar yakin cacar baki tsakanin Amirka da China
Kasashen biyu sun amince cewa China za ta taimaka wajen kawo karshen sarrafa hodar iblis ta fentanyl mai matukar hatsari da ta zama annoba ga Amurkawa.
To amma shugabannin sun yi hannun riga kan batun Taiwan, inda Mr Xi ke cewa babu gudu babu ja da baya kan batun hade Taiwan din da China, kuma lallai Amurka ta dakatar da taimaka wa Taiwan din da take yi da makamai.
Karin bayani:Chaina za ta hada hannu da Rasha don magance rikicin Gaza
Haka zalika shugabannin sun tattauna kan rikicin Gaza da kuma Ukraine, inda ra'ayoyinsu suka bambanta game da bangarorin da suke goyon baya.