Amurka na shirin kawo karshen yakin Sudan
March 27, 2024Amurka ta nuna kyakkyawan fatan kawo karshen yakin Sudan, ta hanyar shirya wata ganawa ta musamman a kasar Saudi Arebiya don cimma yarjejeniyar sulhu.
Wakilin Amurka na musamman a Sudan Tom Perriello, ya ce Washington na da kwarin gwiwar ganin daidaituwar al'amura a wannan ganawa da za a gudanar a ranar 18 ga watan Afirilu mai kamawa, don kawo karshen yakin da ya 'dai'daita miliyoyin mutanen Sudan.
Karin bayani:Al'umma na fuskantar matsalar karancin abinci a Sudan
Ya kara da cewa baya ga Amurka da Saudi Arebiya, su ma masu yaki da juna na daga cikin mahalarta zaman sulhun, sai Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma kungiyar raya kasashen gabashin Afirka wato IGAD.
Karin bayani:Amurka ta koka da matakin sojin Sudan na hana shigar da agaji Darfur
Yakin na Sudan tsakanin sojojin Janar Abdel Fattah al-Burhan da dakarun RSF dake biyayya ga Mohamed Hamdan Dagalo, ya janyo asarar dubban rayukan mutane da kuma raba miliyoyi da muhallansu, baya ga mummunan kangin yunwa.