1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Amurka na zargin Iran da bai wa Rasha makamai

October 13, 2023

Amurka ta gabatar wa Majalisar Dinkin Duniya hujjoji a kan cewa Iran na taimaka wa kawarta Rasha da makamai a mamayar ta take yi wa Ukraine.

https://p.dw.com/p/4XTte
Jarage marasa matuka samfarin Kamikaz kirar Iran
Amurka ta gabatar da hujjon cewa Iran na ba wa Rasha makamaiHoto: Iranian Defence Ministry/AFP

Amurka ta gabatar wa Majalisar Dinkin Duniya wasu tarkacen jirage marasa matuka samfarin Kamikaz kirar Iran, da aka tattaro daga Ukraine a matsayin kwakwarar shaidar cewa Tehran na hulda mai karfi da Rasha a fagen cinikayyar makamai.

A lokacin da aka gabatar da tarkacen, Jakadiyar Amurka da ke Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield ta ce bai wa Rasha makamai domin aikata mugunta a Ukraine abu ne da ya saba wa kudurin kwamitin sulhu na MDD da kuma shirin Tehran na nukiliya.

Karin bayani: Zargin musayar makamai tsakanin Putin da Kim Jong Un

Linda ta kuma ce mahukuntan Tehran ba su boye aniyarsu ba ta fadada cinikayyar makamai da Moscow musanman jirage marasa matuka masu tarwatsewa duk da ce cewa hakan ya saba wa doka, kafin daga bisani ta bukaci hadin kan kasashe domin yi wa tubkar hanci.

Karin bayani: Amurka ba za ta yi watsi da Ukraine ba

An dai share watanni ana zargin Iran da ke da kusanci da Rasha da aikewa dakarun mamayan na Moscow da makamai domin taimaka masu a yakin da suke a Ukraine lamarin da Iran din ke musantawa.