Amurka ta kai sabbin hare-hare kan Houthi a Yemen
January 18, 2024Makaman masu linzami na mayakan Houthi da Amurkan ta lalata an shirya amfani da su ne wajen kai hari kan jiragen ruwan 'yan kasuwa da kuma na sojin ruwan Amurkan da ke shawagi a yankin, a cewar cibiyar bayar da umarnin aiwatar da farmaki na Amurkan a wata sanarwa da ta wallafa a shafin X.
A cewar sojin na Amurka harin zai dakile kaifin hare-haren da mayakan Houthi suka kaddamar kan jiragen ruwan da ke dakon kayan fatauci da kuma na kasa-da-kasa da ke zirga-zirga a Bahar Maliya da zirin Bab-el-Mandeb da kuma gabar tekun Aden.
Mayakan na Houthi sun kaddamar da hare-hare ne kan jiragen ruwa a watan Nuwambar bara domin nuna goyon baya ga al'ummar Falasdinawa da ke Gaza a yakin Isra'ila da Hamas, kuma hakan ya haifar da tsaiko tare da gurgunta kasuwanci tsakanin kasashen Asiya da Turai da jiragen ruwansu ke bin yankin.