1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabon

Amurka ta katse tallafin da take bai wa Gabon

October 24, 2023

Amurka ta sanar da katse tallafin da take bai wa kasar Gabon a wani mataki na yin tir da juyin mulkin da sojoji suka yi wa gwamnatin Ali Bongo a ranar 30 ga watan Ogustan da ya gaba.

https://p.dw.com/p/4XwGQ
Amurka ta katse tallafin da take bai wa kasar Gabon
Amurka ta katse tallafin da take bai wa kasar GabonHoto: AFP/Getty Images

Sai dai a cikin sanarwar da Washington ta fitar ta ce a shirye take da ta canja shawara kan wannan mataki muddin kasar da ke Tsakiyar Afrika ta samu kyakyawan ci gaba a ta fuskar dimokuradiyya.

Karin bayani:Yunkurin maido da tsarin mulki a Gabon

Gabon dai 'yar karamar kasa mai arzikin man fetur na samun tallafin da bai taka kara ya karya ba daga Amurka sabanin sauran kasashen irin su Jamhuriyar Nijar da ta ita ma ta fuskanci juyin mulkin sojoji yau da kusan watanni uku. 

Karin bayani: EU ta kama hanyar kakaba wa Nijar takunkumin karya arziki

Hasali ma a watan Satumba da ya shige a lokacin da yake jawabi a zauren taron koli na Majalisar Dinkin Duniya sabon Firaminstan Gabon din Raymond Ndong Sima ya bukaci kasashen duniya da daina alakanta juyin mulkin da aka yi a kasarsa da na sauran kasashe yana mai cewa sojoji Gabon sun karbe iko ne domin taka birki ga yunkurin yi wa dimukuradiyya karan tsaye.