1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Amurka za ta rama kisan sojojinta da aka yi a Jordan

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
January 29, 2024

Mai magana da yawun majalisar tsaron Amurka John Kirby ya ce wadanda suka aikata hakan za su dandana kudarsu kuma Amurka ba wai tana kokarin haddasa fantsamar rikicin Gabas ta Tsakiya ba ne kuma ba ta neman fada da Iran

https://p.dw.com/p/4boCD
Hoto: Evelyn Hockstein/REUTERS

Amurka ta sha alwashin ramuwar gayya ga wadanda suka kai hari kan sansanin sojojinta a Jordan tare da halaka sojoji uku, inda shugaba Joe Biden ya zargi Iran da hannu a kai, kamar yadda fadar White House ta sanar.

Karin bayani:Iran ta musanta zargin kisan sojojin Amurka

Mai magana da yawun majalisar tsaron Amurka John Kirby ya shaidawa CNN cewa wadanda suka aikata hakan za su dandana kudarsu, kuma Amurka ba wai tana kokarin haddasa fantsamar rikicin Gabas ta Tsakiya ba ne, kuma ba ta neman fada da Iran.

Karin bayani:Isra'ila ta kai sabbin hare-hare a Kudancin Gaza

Tuni dai Iran ta sanar da cewa ba ta da hannu a harin na Jordan.