Iran ta musanta zargin kisan sojojin Amurka
January 29, 2024Hukumomin Iran sun nisanta kansu daga zargin cewa da hannun kasar a hari da jiragi maras matuki wanda ya yi ajalin sojojin Amurka uku tare da jikkatar wadansu 30 a Arewa maso gabashin kasar Jordan. A cikin wata sanawa, kakakin ma'aikatar diflomasiyyar Iran Nasser Kanaani ya ce ana so a goga wa kasar kashin kaji ne domin cimma manufa ta siyasa da nufin kawar da hankula kan abin da ke faruwa a zahiri a yankin Gabas ta Tsakiya in ji shi. Wannan martani na Tehran ya biyo bayan wasu kalamai da jami'in diplomasiyyan Burtaniya David Cameron ya furta, inda ya yi kira ga Iran da ta guji rura rikicin da ake a yankin na Gabas ta Tsakiya.
Karin bayani: Amurka da Burtaniyya sun kai harin bama-bamai kasar Yemen kan 'yan tawayen Houthi
Jim kadan bayan harin na ranar Lahadi 28.01.2024, fadar shugaba Joe Biden ya zargi kungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran, tare da yin barazanar daukar fansa kan masu tsattsauran ra'ayin Islama da suka aikata abin da ya sifanta da aika-aika.
Wannan dai shi ne karon farko da aka kashe sojojin Amurka a yankin Gabas ta tsakiya tun bayan barkewar sabon rikici tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas a Zirin Gaza.