1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Takarar Biden na kara fuskantar barazana

July 13, 2024

Yayin da zaben shugaban Amurka ke karatowa wasu manyan jiga-jigai a jam'iyyar Democrat sun kara nuna adawa ga takarar shugaba Joe Biden yayin da shi kuma ke cewa babu gudu babu ja da baya.

https://p.dw.com/p/4iFH6
Takarar Biden na kara fuskantar barazana
Takarar Biden na kara fuskantar barazanaHoto: Justin Sullivan/Getty Images

Tsaffin 'yan majalisar wakilan Amurka na jam'iyyar Democrat sama da 20 sun wallafa wata wasika a ranar Juma'a suna masu neman Shugaba Joe Biden da ya kira babban taron tattaunawa da 'ya'yan jam'iyyar domin bai wa sauran masu sha'awar tsayawa takara a zaben kasar na watan Nowamba damar gabatar da kansu.

Karin bayani: Biden: "Babu guda babu ja da baya a tsayawa takara"

A  cikin budadiyar wasikar, staffin jiga-jigan jam'iyyar ta Democrat sun ce idan har mista Biden na son hidimtawa Amurka ya zama wajibi ya dakatar da yunkurin yin gaban kansa domin barin wakilan jam'iyyar sun ayyana shi a matsayin wanda zai tsaya takara a karo na biyu.

Wasikar ta kuma ce mutumcin shugaban da hangensa na nesa na jagoranci bai disashe ba, amma kuzari da karfin da yake bukata domin gudanar da yakin neman zabe har ma da jan ragamar Amurka a wa'adin mulki na biyu sun ragu.

Karin bayani: Biden da Trump sun caccaki juna a wajen muhawara

Tun bayan mahawarar da ya yi da abokin hamayarsa Donald Trump, Shugaba Joe Biden mai shekari 81 a duniya ke fuskantar zazzafar suka daga makusantansa tare da kiransa da ya janye daga tsayawa takara, yayin da shi kuma ke cewa babu gudu babu ja baya.