1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biden da Trump sun caccaki juna a wajen muhawara

June 28, 2024

Shugaba Joe Biden na Amirka ya bude muhawarar da kafar CNN ta shirya da dora wa Shugaba Trump alhakin haifar da koma baya ga tattalin arzikin kasar a zamanin mulkinsa.

https://p.dw.com/p/4hcTN
Biden da Trump sun caccaki juna a wajen muhawara
Biden da Trump sun caccaki juna a wajen muhawaraHoto: Mike Blake/REUTERS

Muhawarar da ta gudana tsakanin shugaban Amirka Joe Biden da kuma abokin hamayyarsa, Donald Trump ya sanya fara aza ayar tambaya a tsakanin 'yan jam'iyyarsa kan ko a maye gurbin Shugaba Biden da wani da zai tsaya takara a babban zaben kasar na watan Nuwambar, sakamakon yadda ya rika hardewa da kuma kasa kare maganarsa a yayin muhawarar.

Shugaba Biden dai ya bude muhawarar da kafar CNN ta shirya, da dora wa Shugaba Trump alhakin haifar da koma baya ga tattalin arzikin Amirka a lokacin da ya karbi mulki inda mutane da dama suka dandana kudarsu.

Karin bayani: Trump da Biden sun yi muhawarar karshe

Sai dai kuma Trump ya mayar da martanin shi ma, inda ya zargi gwamnatin Biden da rashin gudanar da shugabanci na gari yana mai cewa, matsalar tsadar rayuwa na kashe su. Shugaba Trump dai ya yi ta furta kalamai da zarge-zarge a lokuta da dama ba tare da bayar da shaida ba, kana ya yi ta wasa kansa. Ko a kan yakin Ukraine ma, shugabanin sun yi ta musayar kakkausar kalamai a tsakaninsu, inda Trump ke ganin cewa Shugaba Biden na wuce makadi da rawa wajen bayar da tallafin yaki ga Ukraine din.