An bankado malamai na ci da gumin gwamnati a Sokoto
May 23, 2024Kwamitin ya ga halin da wata makaranta Sakandare ta ke ciki da malamai kusan 30 ne kawai ke zuwa koyar da darasi a makarantar daga cikin malamai 98 da makarantar take da su, kana kwamitin ya hakikance galibin malaman makarantar da ba sa zuwa zuwa karantarwa matan manya ne da kuma 'ya'yan masu fada aji a Najeriya.
Wannan lamari ya sanya ilimin makarantun Firamari da Sakandare da ke karkashin kulawar gwamnati fuskantar koma baya, sai dai kwamitin ya ce shugabannin makarantun sun tabbatar masa da cewa sun sha kai korafi amma saboda galihu da ke ga wasu malaman ba bu wani mataki da aka dauka akai.
Shugabannin kwamitin sun nuna fargaba kan irin yadda makomar ilimin arewacin Najeriya za ta kasance idan aka yi la'kari da halin da rikon sakainar kashi da wasu malamai ke yi wa harkar Ilimi a arewacin Najeriya.