1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya ta bude iyaka da Jamhuriyar Nijar

March 13, 2024

Wani juyin mulki a bangaren sojojin Jamhuriyar Nijar ya janyo saka takunkumi ga kasar daga kasashen yankin yammacin Afirka sakamakon matakin kungiyar kasashen yankin da Najeriya take jagoranci.

https://p.dw.com/p/4dTsH
Iyaka tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar
Iyaka tsakanin Najeriya da Jamhuriyar NijarHoto: Mohammed Babangida/AP/dpa/picture alliance

 

A watan Fabrairun da ya shude wani taro na kasashen yankin yamamcin Afirka na kungiyar ECOWAS ya umarci dage takunkumin da komawa tattaunawa da nufin kai karshen takkadamar da kasashen kawayen Sahel. Wata sanarwar fadar gwamnatin Najeriyar dai ta aiwatar da umarnin ECOWAS din tare da bude daukacin iyakokin da ke tsakanin kasashen guda biyu, ko bayan dage haramcin amfanin sararin samaniya bisa jiragen jigila.

Karin Bayani: ECOWAS ta dage wani bangaran takunkumin da ta saka wa Nijar

Najeriyar dai a cewar sanarwar ta kuma dage takunkumin hada-hadar kudi da samar da wutar lantarki. Haka kuma an dage haramcin taba kaddarorin Jamhuriyar Nijar da ke bankin yammacin Afirka. Su kansu jami'an gwamnatin Jamhuriyar Nijar da iyalansu a cewar mahukuntan Najeriya suna da 'yancin zirga-zirga ya zuwa Najeriya.