Jamusawa na zaben shugaban gwamnati
September 26, 2021Kuri'ar jin ra'ayin jama'a tuni ta nuna cewa dan takarar jam'iyyar SPD Olaf Scholz shi ne zai lashe zabe da d'an karamin rinjaye. Sai dai a ranar Asabar, babban mai adawa da shi, wato Armin Laschet na jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ya samu goyon bayan shugabar gwamnati a wurin kammala yakin neman zabe. Hakan kuma ya kara wa Laschet din tagomashi. Akwai kuma Annalena Baerbock, wace ke yi wa jam'iyyar The Greens mai fafatukar kare muhalli takara, wadda a baya-bayan nan ita ma tauraruwarta ta fara haskawa.
Mutane sama da miliyan 60 ne ake sa ran za su kada kuri'arsu. Sai dai Jamusawa ne kawai aka amince su kada kuri'a a zaben. Amma wasu 'yan kasashen waje da suka samu shaidar zama 'yan kasa, su ma za su kada kuri'arsu kamar Jamusawa, yayin da wadanda ba su da shaidar zama dan kasa ke bayyana ra'ayoyinsu ta hanyar gangamin siyasa daban-daban. Da karfe 6 na yamma agogon Jamus ake sa ran rufe runfunan zaben, koda yake wasu ma sun riga sun kada kuri'arsu ta hanyar gidan waya.