1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dage zaben Najeriya zuwa watan Maris

Salisou BoukariFebruary 8, 2015

Hukumar zaben Najeriya ta dage zaben shugaban kasar zuwa ranar 28 ga watan Maris saboda dalilai na rashin tsaro da ake fama da su a wasu sassan kasar.

https://p.dw.com/p/1EXqm
Hoto: AP

Hukumar zaben Najeriya INEC, ta sanar da dage zaben shugaban kasa da na 'yan Majalisun dokoki ya zuwa ranar 28 ga watan Maris mai zuwa, a wani abin da ke zama bada kai bori ya hau dangane da kiraye-kirayen da aka yi ta yi mata na ta dage wannan zabe saboda dalillai na tsaro. A yammacin ranar Asabar ne dai Shugaban hukumar zaben mai zaman kanta a Najeriya, Farfesa Attahiru Jega ya fitar da wannan sanarwa ga manema labarai, inda ya ke cewa sun dage wannan zabe ne dangane da bayanan da suka samu bisa fannin na tsaro tun da harkokin tsaro ba ya karkashin hukumarsa ta zabe.

Farfesa Jega dai ya ci gaba da cewa, idan dai har ma'aikatan kula da harkokin zabe, da ma 'yan kallo na kasashen waje da suka zo domin zaben ba su da kyaukyawan tsaro, sannan ga rayuwar dumbun matasa da mata da ke cikin hadari, da ma kayan zaben kansa, don haka wadannan abubuwa muka hango cewa za su iya kawo nakasu ta yadda ba za a iya samun ingantaccen zabe ba. Da ma dai a kwanakin baya mai bada shawara kan harkokin tsaro a Najeriya Sambo Dasuki ya nemi da a dage wannan zabe har ya zuwa makonni shidda nan gaba.