1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dage zaman majalisun dokokin Najeriya

Mohammad Nasiru AwalNovember 20, 2014

Shugaban majalisar dattijan Najeriya ya soke zaman majalisun dokokin kasar bayan wata hayaniya a zauren majaliar wakilai.

https://p.dw.com/p/1DqkQ
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Shugaban majalisar dattijan Najeriya Sineta David Mark ya ba da umarnin rufe majalisun dokokin kasar bayan wani hargitsi da ya faru a majalisar wakilai lokacin da 'yan sanda suka harba hayaki mai sa hawaye, a kokarin hana kakakin majalisa Aminu Waziri Tambuwal shiga zauren majalisar, inda zai jagoranci muhawara game da bukatar tsawaita dokar ta baci a wasu jihohi uku na arewa maso gabacin Najeriya. Sineta David Mark ya ce sai mako mai zuwa majalisun za su koma aiki.

"Na yanke shawarar rufe majalisar dattijai da ta wakilai har zuwa ranar Talata. Za mu gaiyaci sifeto janar na 'yan sanda a ranar Talata. Kun san cewa mun nemi shugabannin 'yan sanda su zo nan wurin kuma sun zo a wannan safiyar. Na yi magana da su kuma na ce su dawo ranar Talata. Saboda haka ba bu zaman majalisun dokokin kasa har mako mai zuwa."

Da dai a wannan Alhamis 'yan majalisar wakilai za su tattauna a kan bukatar tsawaita dokar ta baci da shugaban kasa ya gabatar.