Burikina Faso: Traore ya tsallake rijiya da baya
September 28, 2023A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar Burkina Faso ta fidda, ta sanar da kama jami'ai da dama da kuma wadanda ake zargi da hannu a wannan yunkuri na ta da zaune tsaye tare da jefa kasar cikin rudani, sannan kuma ana ci gaba da farautar karin wadansu mutane.
Karin bayani: Burkina Faso: An kama wasu sojoji
Da yammacin ranar Talata 26.09.2023 dai dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a Ouagadougou babban birnin kasar suna masu jaddada goyon baya ga shugaban mulkin sojan kasar jim bayan da aka samu yaduwar jita-jita a kan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.
Karin bayani: Kyaftin Traoré: "karfin abokan gaba ya karu"
Wannan yunkurin juyin mulki dai na zuwa ne shekara guda bayan darewar Kyaftin Ibrahim Traore kan karagar mulki bayan da ya hambarar da gwamnatin sojan waccan lokaci karkashin laftanal Kanal Paul Henri Sandaogo Damiba.