Kotu a Masar ta yanke wa madugun 'yan adawa hukuncin dauri
September 16, 2023Wata kotu a Masar ta yanke wa madugun 'yan adawan masu sassaucin ra'ayi Hicham Kassem hukuncin dauri na watanni shida a gidan yari, abin da ka iya haramta masa gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa wanda da za a yi a watanni masu zuwa.
Karin Bayani: Kyakkyawan fata bayan shigar Masar a BRICS
Wata majiya daga makusantan dan siyasan ta ce an yankewa Hicham hukuncin zama a gidan wakafi na watanni uku, tare da cinsa tarar kudi Yuro 600 bisa zarginsa da yin kalaman karya kan wani minista a lokacin da ya gurfana a gaban kotu.
Karin Bayani: Haramcin sanya nikabi a makarantun Masar
Tuni lauyan da ke kare dan siyasa Nasser Amin ya sanar da daukaka kara kan hukuncin, inda ya ce za a sake zaman shari'ar a farkon watan Oktoba. Wannan dai ba shine karon farko da wani dan adawa a Masar ke fuskantar shari'a ba tun bayan da aka buga kugen siyasa a kasar.