Me ke kashe mutane a Kano?
April 23, 2020Sani Aliyu jami'in da ke jagorantar kwamitin yaki da coronavirus a kasar ne ya tabbatar da haka ga kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Aliyu ya ce gwamnati na karbar bayanan mamatan don gano ko cutar coronavirus ce ta yi ajalinsu. A ranar Talata wata jarida a Najeriya ta ruwaito cewa akalla mutane 150 suka mutu a birnin Kano a cikin kankanin lokaci. Sai dai babu wanda zai iya tabbatar da ko coronavirus ce tayi ajalinsu ko kuma a'a.
Bayanai na karshe daga gwamnatin Najeriya na nuni da cewa akwai mutane 873 da suka kamu da corona a kasar. A cikin wannan adadin mutum 73 na jihar Kano, kuma gaba daya a kasar mutum 197 suka warke yayin da cutar ta yi ajalin mutum 28.
A wannan Alhamis dai gwamnoni 36 na kasar sun ce za su sanya dokar hana zirga-zirga wace za ta hana duk wata hada-hada da ba ta zama dole ba a jihohin kasar. Matakin da suka ce na tsawon makonni biyu ne ana fata ya dakile bazuwar corona wace ke ci gaba da bulla a jihohin kasar.