An bude rufunan zaben shugaban kasa a Aljeriya
September 7, 2024Fiye da 'yan Aljeriya miliyan 24 sun fita rufunan zabe a ranar Asabar domin kada kuri'ar zaben shugaban kasa, wanda ake sa ran shugaba mai ci Abdelmadjid Tebboune zai lashe domin ci gaba da jan ragamar kasar a wa'adin mulki na biyu.
Karin bayani: Jam'iyyar FLN ta kama hanyar lashe zabe
An bude runfuna zaben da kimanin karfe shida na safiya agogon GMT, kuma za a fara samun sakamakon farko da maraicen Asabar, kana ana sa ran fidda sakamako a hukumance a ranar Lahadi.
'Yan takara biyu ne dai bakin fuskoki a fagen siyasar Aljeriya ke kalubalantar shugaba mai ci Abdelmadjid Tebboune a zaben na ranar 07.09.2024, da suka hadar da Abdellahi Hassani mai shekaru 57 na babbar jam'iyyar Islama ta MSP da kuma Youcef Aouchiche mai shekaru 41 tsohon dan jarida kuma sanata daga jam'iyyar adawa mafi tsufa a kasar.
Gabanin zaben dai kungiyar kare hakkin da Adam ta Amnesty International ta gargadi gwamnatin Aljeriyar a game da danne 'yancin walwalar jama'a da kuma kame-kamen 'yan siyasa ba bisa ka'ida ba, wannan ne ma ake tunanin zai iya haifar da raguwar wadanda za su fita rufunan zabe.