1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

An fara shari'ar Donald Trump kan zargin bada toshiyar baki

April 22, 2024

Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana a gaban kotun Manhattan da ke birnin New York na Amurka, kan zargin bai wa wata fitacciyar 'yar fina-finan batsa toshiyar baki.

https://p.dw.com/p/4f3qH
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump a wani zaman kotun Manhattan na Amurka
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump a wani zaman kotun Manhattan na AmurkaHoto: Jabin Botsford/REUTERS

Masu gabatar da kara suna can suna bayyana masa dalilan da suka sa kudaden da ya bai wa wata fitacciyar mai fina-finan batsa a matsayin toshiyar baki ya zama laifi da kuma karya doka.

Karin bayani: Donald Trump zai gurfana a gaban kotu

Donald Trump dai shi ne shugaban kasar Amurka na farko da ya ke fuskantar shari'a a gaban kotu kan wani babban laifi irin wannan; su ma lauyoyin Trump za su gabatar da nasu bayanan a gaban kotu domin kare shi daga laifin da tuni ya musanta.

Karin bayani: Kotun kolin Amurka ta bai wa Trump damar tsayawa takara

An yi zargin tsohon lauyan Trump Michael Cohen ne ya bada kudin dala $130,000 ga  Stormy Daniels a matsayin toshiyar baki don kar ta fallasa a bin lalatar da ta shiga tsakaninta da Trump.