1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

An fara zaben wuri a Amurka

September 10, 2024

Masu zabe a Amurka sun fara zaben wuri domin mutanen da suke rayuwa nesa da mazabunsu, gabanin zaben kasa baki daya da za a gudanar a farko watan Nuwamba.

https://p.dw.com/p/4kT4T
Zaben Amurka
Zaben AmurkaHoto: Evelyn Hockstein/REUTERS

Dan takarar Shugabancin kasar Amurka na Jam'iyar Republican Donald Trump ya sake zargin da ya dade yana yi wa ‘yan Demokrats cewa, suna kokarin yin amfani da baki ‘yan-cirani  a zaben watan jibi na Nuwamba, dan cimma burinsu na lashe zaben. Wannan lokacin da masu zabe a Amurka sun fara zaben wuri, wanda aka bai wa mutane dama musamman wadanda suke rayuwa a wajen kasar gami da n mutanen da suke rayuwa nesa da mazabunsu. Yayin da wasu kuma suke ganin zargin a matsayin cin-fuska ne da raunana Demokradiyyar kasar, da 'yar takarar jam'iyyar mataimakiyar shugabar kasar Kamala Harris. Yanzu haka 'yan takarar biyu da ke neman shugabancin Amurka za su fafata a muhawara.

Karin Bayani: Trump da Harris na shirin tafka mahawara kan manufofinsu

Muhawara a zaben Amurka na 2024
Muhawara a zaben Amurka na 2024Hoto: Pablo Martinez Monsivais/picture alliance

Ga masu bibiyar al'amuran siyasar Amurka, zargi na yin magudi a zabe ba wani sabon abu ne musanman daga bakin Donald Trump, amma illa ko tasirin irin wadannan kalamai daga tsohon Shugaban kasar, su ne abun damuwa. Dan takarar na jam'iyyar Republican ya cigaba da zargin cewa, wannan zai iya shafar zaben na watan Nuwamba, wani lamari da za a iy fassarawa da cewa Trump, ya aza harsashin jefa shakku da rikici ke nan a zaben, musanman idan aka tuna yadda irin wadannan karerariya na Trump suka tunzura wasu magoya bayansa suka kai hari ga majalisar dokoki a lokacin tabbatar da kayen da Joe Biden ya yi masa a zaben shekara ta 2020.