An fasa tafiya yajin aiki a Najeriya
September 28, 2020Talla
Kungiyoyin dai sun tsara yajin aikin ne saboda turje wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, wadda ta dauki matakin janye tallafi kan makamashin man fetur da na wutar lantarki, abin da ya janyo tsanantar halin rayuwa a Najeriyar a yanzu.
A makon jiya ne babbar kungiyar kwadago ta NLC da ke wakiltar miliyoyin ma'aikata a kasar da ta fi kowacce karfin tattalin arziki a Afirka, ta sanar da shirin fara yajin aikin a yau Litinin.
Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari, ya ce kasar ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin ba, dole ne a bar kasuwa ta yi alkalanci, amma kungiyar kwadagon ta kekashe kasa ta ce lallai ne a dawo da farashin mai da wutar lantarki, muddin hukumomin na son sansatawa da ita a kan yajin na aiki.