An gana tsakanin ministan harkokin wajen Iran da na Jamus a Berlin
June 24, 2006Talla
Ministan harkokin wajen Iran Manoucher Motaki ya gana da takwaran aikinsa na Jamus Frank-Walter Steinmeir a birnin Berlin, inda suka tattauna akan shirin nukiliyar Iran da ake takaddama akai. Mottaki ya bayyana taron da suka yi da cewa ya yi armashi, to amma ba za´a iya matsawa gwamnatinsa a birnin Teheran lamba ba. Jamus da sauran kasashe 5 dake da kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD na jiran amsa ga tayin taimakon tattalin arzikin da suka yiwa Iran idan ta dakatar da aikace aikacen inganta sinadarin uranium. Gwamnatin birnin Teheran ta ce a cikin watan agusta zata mayar da martani ga tayin, amma KTT da Amirka sun yi kira da tas yanke shawara kafin wannan lokaci.