1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanci

An gargadi Najeriya kan yiwuwar kai hari

Uwais Abubakar Idris MAB
October 24, 2022

Sanarwar da ofisohin jakadancin Amirka da Birtaniya da Italiya suka fitar kan yiwuwar kai hare-haren ta’adanci a Abuja babban birnin Najeriya ta haifar da martani da zaman zullumi duk da matakan tsaro da ake kara dauka .

https://p.dw.com/p/4IcC0
'Yan ta'adda sun taba kai harin bam a Wuse da ke birnin Abuja na NajeriyaHoto: DW/K. Gänsler

Ba kasafai wadannan ofisoshin jakadancin Amirka da Birtaniya da Italiya ke fitar da sanarwa iri guda kuma a kan batu iri daya na yiwuwar kai hare-haren ta'adanci a Abujan babban birnin Najeriya ba. Saboda haka ne ta sanya tambayoyi a kan dalilin yin hakan da abin da suka gani. Hasali ma sun ja hankalin ‘yan kasarsu da ke Najeriyar da su yi taka-tsantsan a kan wuraren da suke zuwa, tare da daukar matakai. Sun ma zayyana wurare da dama da suka ce za'a iya kai harin ta'adanci a Abujan da suka hada da manyan shaguna da wuraren taron jama'a da wuraren ibada da hotal.

Der nigerianische Vizepräsident Yemi Osinbajo
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo lokacin da ya dauki bakuncin Antony BlinkenHoto: Andrew Harnik/ASSOCIATED PRESS/picture alliance

Wadannan jakadu sun ja hankali ga ‘yan asalin kasashensu da ke zaune a Najeriyar, amma sako ne da ke da amfani ga daukacin mutanen da ke zaune a Najeriyar da ma hukumomin tsaro wadanda za'a ce sun samu bayanai na sirri da sukan yi kukan rashin su na zama cikas.

Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriyar watau DSS ta mayar da martani a kan wannan sanarwa da ta sanya ‘yan Najeriya da dama ciki yanayi na zullumi. A sanarwar da jami'in yada labaru na hukumar Dr Peter Afunanya ya sanya wa hannu, hukumar DSS ta bukaci mazauna Abuja su kwantar da hankalinsu domin tana aiki da sauran hukumomin tsaro.

Nigeria Armee Anschlag in Abuja 25.6.2014
Jami'an tsaron Najeriya sun tsaurara matakan kare mazauna Abuja daga hariHoto: REUTERS

Akwai alamu daukan karin matakan tsaro a Abuja musamman a hanyoyin shiga birnin da ma wuraren gudanar da tarurruka.