1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gina makarantar marayu a Katsina

Yusuf Ibrahim Jargaba | Abdul-raheem Hassan
November 8, 2017

Ma'aikacin gwamnatin Tarayyar Najeriya, ya sadaukar da kudin garatutinsa wajen gina makaratar marayu da marasa galihu. Mutumin ya yi la'akari da nisan hanya da ke hana yara zuwa karatu a kan lokaci.

https://p.dw.com/p/2nHHw
Nigeria Makoko schwimmende Schule in Lagos
Hoto: Reuters/A. Akinleye

Aliyu Babajo funtuwa da ke a yankin karamar hukumar Funtuwa a jihar katsina, ma'aikacin gwamnatin Tarayya ne da ya aji ye aiki kuma ya yi amfani da kudin sallamarsa wajen bada gudummuwa ta fuskar ilmi. Inda ya gina wata makarantar Boko dan tallafa wa marayu da yayan marasa karfi.

Yara da dama ba sa samun damar zuwa makaranta saboda nisan hanya, sannan talauci na taka rafwa wajen hana iyayen yaran samun damar sayamusu abun hawa da zai rage hanya. A yanzu dai dalibai marayu da yayan marasa galihu da dama sun amfana da wannan makaranta, inda a yanzu wasu daliban sun samu damar zuwa matakin karatun gaba da sakadare.