1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun yi barna a Benue

Zainab Mohammed Abubakar
April 7, 2023

'Yan bindiga sun kai hari a wani kauye a yankin Arewa maso tsakiyar Najeriya, inda suka kashe mutane masu yawa.

https://p.dw.com/p/4Pp1b
'Yan sandan NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Harin da ya faru a ranar Laraba a ritsa ne da al'ummomin Umogidi da ke jihar Benue, inda ake yawan samun tashe-tashen hankula tsakanin makiyaya da manoma da ke neman filaye da albarkatun kasa.

Mai baiwa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro Paul Hemba, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, an samu ceto gawarwakin mutane 46 daga cikin wadanda aka kashe, kuma har yanzu ba a san inda wasu suke ba.

Ya zargi makiyaya da kai harin, kamar yadda suka sha kai wa al'ummomin yankin a cikin watan da ya gabata. Ya zuwa yanzu dai ba a fayyace dalilin kai harin ba, amma Benue na daya daga cikin wuraren da rikicin manoma da makiyaya ya fi kamari a Najeriya.