1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An harba wa 'yan majalisar dokokin Najeriya barkonon tsohuwa

Mohammad Nasiru AwalNovember 20, 2014

Hakan ya faru ne lokacin da kakakin majalisar da tawagarsa suka isa don kada kuri'a a kan bukatar tsawaita dokar ta baci.

https://p.dw.com/p/1DqL7
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Dakarun tsaron Najeriya, sun harba hayaki mai sa hawaye a cikin harabar majalisar dokokin kasar a daidai lokacin da 'yan majalisa na bangaren adawa cikin har da kakakin majalisar wakilan Aminu Waziri Tambuwal suka isa don kada wata muhimmiyar kuri'a a kan dokar ta baci a yankin arewa maso gabashin kasar. Wakilinmu a Abuja Uwais Abubakar Idris da sauran 'yan jaridar da suka shaida lamarin sun ce babban zauren shiga majalisar ya cika da hayakin barkonon tsohuwar da 'yan sanda suka harba a lokacin da kakakin majalisar Aminu Tambuwal wanda a watan da ya gabata ya canja sheka zuwa babbar jam'iyyar adawa ya shiga cikin ginin. Ofishin Tambuwal ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma kakakin 'yan sanda Emmanuel Ojukwu ya musanta cewa da hannun jami'an 'yan sanda a ciki. Kakakin majalisar dai ya umarci dukkanin 'yan majalisar su dawo daga hutu a wannan Alhamis domin tattaunawa a kan bukatar tsawaita dokar ta baci da shugaban kasa ya gabatar.