1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kalubalanci sakamakon zaben Najeriya

Suleiman Babayo AH
March 21, 2023

Peter Obi ya garzaya kotu inda kalubalanci sahihancin sakamakon zaben shugaban kasa na Najeriya wanda jam'iyya mai mulki ta APC ta samu galaba.

https://p.dw.com/p/4P0zo
Najeriya lokacin yakin neman zaben
Peter Obi dan takara a zaben shugaban kasa na NajeriyaHoto: Katrin Gänsler/DW

Daya daga cikin 'yan takara a zaben shugabancin Najeriya da ya gudana a watan jiya na Febrairu, Peter Obi wanda ya zo na uku ya shigar da kara a hukumanci domin kalubalantar sahihancin sakamakon zaben. Mai magana da yawun jam'iyyar ma'aikata ta Labour Party a Najeriya wadda Peter Obi ya yi takara karkashinta, ya ce a wannan Talata suka shigar da kara.

Shi dai Obi ya zo na uku lokacin zaben wanda hukumar zabe ta ayyana Bola Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya samu nasara, kana Atiku Abubakar na babbar jam'iyyar adawa ta PDP ya zo na biyu.

A Najeriyar ana ci gaba da samun sakamakon zabe gwamnoni 28 daga cikin 36 da aka yi a karshen mako, inda zuwa yanzu APC mai mulki ta samu jihohi 15 da suka hada da Lagos, Sokoto, Katsina, Jigawa, Gombe, Kwara, Niger, Yobe, Nasarawa, Cross River, Ebonyi, Ogun, Benue, Kaduna da Borno.

Ita kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta samu jihohi takwas da suka hada da Plateau, Bauchi, Oyo, Delta, Rivers, Akwa Ibom, Taraba da Zamfara. Sannan jam'iyyar adawa ta NNPP ta lashe jihar Kano cibiyar kasuwancin arewacin kasar. Ba a kammala zabe a jihohin Adamawa da Kebbi ba.