An kama wadanda suka sace 'yan Chibok
July 18, 2018Talla
'Yan sanda a Najeriya, sun ce an kama wasu mutane takwas da ake zarginsu da hannu cikin sace 'yan matan makarantar Chibok sama da 200 shekaru hudun da suka gabata, a yankin arewa maso gabashin kasar.
A cewar jami'an 'yan sandan, mutanen takwas na cikin wasu 'yan Boko Haram 22 din ne da ake tsare da su wadanda kuma aka soma bincike kansu tun bara.
Akwai ma wasu mutum 14 da ake zarginsu da kasancewa cikin wadanda ke kitsa hare-haren kunar bakin wake da kuma taimaka wa ayyukansu na zirga-zirga.
Yayin da ake gabatar da su gaban 'yan jaridu a wannan Larabar a Maidugurin jihar Borno, kwamishinan 'yan sandan jihar Damian Chukwu, ya ce mutanen wadanda ke tsakanin shekaru 20 zuwa 48, dukkaninsu sun fito ne daga garin Bama da ke jihar ta Borno.