1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kara kudin wutar lantarki a Najeriya

Uwais Abubakar Idris M. Ahiwa
June 26, 2023

A Najeriya an kama hanyar fuskantara fito-na-fito a tsakanin kungiyoyin kwadago da gwamnati, bayan sanar da karin farashin wuta lantarki da kaso 40 cikin 100.

https://p.dw.com/p/4T5AN
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Jallanzo

Takaddama ta kuno kai biyo bayan sanarwar da kamfanonin da ke sayar da wutar lantarki suka fitar da sanarwar cewa ‘yan Najeriya su saurari kari na farashin lantarki farawa daga watan gobe na Yuli, karin da ta bayyana ya kai na kashi 40 cikin 100 na farashin da ake sayar da wutar a Najeriyar. Sun bayyana cewa ya zama dole ne su yi karin saboda tangal-tangal da takardar kudin Najeriyar ta Naira ke yi.

To sai dai da safiyar wannan Litinin kamfanain sayar da wutar lantarki na Abuja ya bayyana cewa har yanzu ba su samu amincewar gwamnati a kan karin ba. Tuni dai kungiyoyin kwadagon Najeriya suka yi watsi da wannan kari.

Ana shirin gudanar da wannan kari na farashin wutar ne a daidai lokacin da samun makamshin ya yi wahala a wasu sassan Najeriya. Karin kudin wutar lantarki na neman zama dan kullum a Najeriyar, domin sau uku a cikin shekaru biyar ana karin bisa dalilai mabambanta.

Karin na lantarki dai shi ne na baya-baya a jerin kare-karen abubuwa da gwamnatin shugaban Najeriyar karkashin jagoranci Bola Ahmed Tinubu take yi.

A yayin da kungiyar kwadagon Najeriyar ta yi barazanar shiga yajin aiki, kamfanonin sayar da wutar ba za su sauya aniyarsu ba. A baya dai gwamnatin ta samu nasarar shan gaban ‘yan kwadgon, inda ta dakatar da yunkurinsu na shiga yajin aiki ta amfani da karfin shari’a a kotun kasar. Shin sun kama hanyar zama magen lami ne ko suna da sauran katabus?