An kashe shugaban Hamas Ismail Haniyeh a Iran
July 31, 2024A cikin sanarwar da rundunar juyin-juya hali ta Iran (IRGC) ta fitar, ta ce Ismail Haniyeh ya gamu da ajalinsa tare da dogarinsa guda a wani hari da aka kai kan gidansa a birnin Tehran.
Karin bayani: Jagoran Hamas Ismail Haniyeh ya isa Masar kan rikicin Gaza
Rundunar ta kara da cewa, a yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike inda a gaba za a fitar da karin bayani. A cikin sanarwar da kungiyar Hamas ta fitar, ta ce shugabanta, Haniyeh ya rigamu gidan gaskiya ne bayan da ya halarcin bikin rantsar da sabon shugaban kasar Iran.
Ismail Haniyeh ya shiga kungiyar Hamas a shekarar 1987, a lokacin da aka kafata yayin gudanar da wani gagarumin bore ga Isra'ila. A shekarar 2006 ya zama firanministan Falasdinu, duk da cewa bangarorin da ke hamayya sun yi ja-in-ja kan sahihancin matsayinsa na tsawon shekaru.
Karin bayani: Hamas ta zabi Isma´il Haniyeh a matsayin saban Pramistan Palestinu
An kuma zabe shi a matsayin shugaban kungiyar Hamas a shekarar 2017. Shugaban na Hamas na gudun hijira ne a kasashen Katar da Turkiyya tun a shekarar 2016. A watannin baya-bayan nan ya yi ganawar diflomasiyya da manyan shugabanin siyasa a kasashen biyu.