Najeriya: An kashe 'yan sanda 25 a rikicin ENDSARS
October 30, 2020Rundunar 'yan sandan Najeriya ta fitar da sanarwa a wannan Juma'a kan ta'asar rikicin dandalin Lekki na jihar Legas. Mai magana da yawun rundunar Frank Mba, ya ce jami'anta akalla ashirin da biyu ne suka mutu a yayin da aka kona ofisoshin 'yan sanda kimanin dari biyu da hamsin, alkaluman na tsawon lokacin da aka kwashe ne ana zanga-zangar ENDSARS a cikin watan Oktoba a kasar.
Jami'in ya kara da cewa, akwai karin jami'an da suka ji rauni, wasunsu yanzu suna kwance a asibiti a cikin mawuyacin hali. Mista Mba, ya ce jami'an sun rasa rayukansu a yayin da suke kokarin tabbatar da zaman lafiya duk kuwa da barazanar da rayukansu ke ciki a lokacin boren.
Sai dai, bai ce komai ba, kan zargin jami'an da aka yi da laifin kisan masu zanga-zangar a yayin jawabin nasa. Amma rahotannin da suka yi ta karo da juna dai, sun zargi jami'an da soma bude wuta kan masu zanga-zangar, lamarin da aka ce, ya yi sanadiyar rayukan fararen hula sama da hamsin, batun da rundunar ta musanta.