SiyasaZimbabwe
An rantsar da shugaban Zimbabuwe a wa'adi na biyu
September 4, 2023Talla
Mr. Mnangagwa wanda ya yi alkawarin tsame miliyoyin 'yan kasar ta Zimbabuwe daga talauci, ya yi nasara ne a zaben ranar 23 ga watan jiya, zaben da ake tababa a kansa.
A jawabin da ya gabatar bayan shan rantsuwa a yau din, shugaban na Zimbabuwe ya bukaci hadin kan 'yan kasar tare da alkawarin sake zaburar da harkokin tattalin arziki.
Alkalin alkalan Zimbabuwe Luke Malaba da ya bayyana Shugabab Mnangagwa a matsayin wanda ya ci zabe a kotu a 2018, shi ne ya rantsar da shi a wa'adin na biyu.