1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun rufe iyakokin Jamhuriyar Nijar ta sama

Suleiman Babayo MAB
August 7, 2023

Sojojin da suka kwace madafun ikon kasar Jamhuriyar Nijar sun rufe iyakokin kasar ta sama byan wa'adin da kungiyar ECOWAS ta bai wa sojoji na ajiye madafun iko ya cika.

https://p.dw.com/p/4UqNh
JAmhuriyar Nijar, birnin Yamai | Janar Abdourahmane Tchiani wanda ya jagoranci juyin mulki
Janar Abdourahmane Tchiani lokacin gangami a birnin YamaiHoto: Balima Boureima/AA/picture alliance

Sojojin da suka kwace madafun ikon kasar Jamhuriyar Nijar sun rufe iyakokin kasar ta sama bisa abin da suka kira barazanar kutse, bayan wa'adin da kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS/CEDEOA ya cika na mayar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoun da sojojin suka yi wa juyin mulki.

A wannan Lahadi da ta gabata wa'adin mako guda na mayar da kasar bisa tafarkin tsarin mulki ya cika, bayan juyin mulkin da sojojin suka yi.

Ita dai kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ta sha alwashin bin duk matakan da suka dace wajen ganin sojojin sun yi sallama da madafun ikon kasar ta Jamhuriyar Nijar. Abin jira a gani shi ne mataki na gaba da kunguyar ECOWAS za ta dauka karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya, bayan cikar wa'adin.

Tuni dai Antonio Tajani ministan harkokin wajen Italiya ya bukaci kungiyar ta ECOWAS/CEDEOA ta tsawaita wa'adin da ta bai wa sojojin da ke rike da ragamar Jamhuriyar Nijar, saboda yuwuwar samun mafita yayin hira da aka wallafa a wannan Litinin a wata jaridar kasra ta Italiya mai suna La Stampa.