1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu jinkirin isar jami'an zabe a wasu rufuna

Mohammad Nasiru Awal MAB
February 25, 2023

Miliyoyin masu zabe sun fita kada kuri'a, inda za su zabi sabon shugaban kasa da 'yan majalisun wakilai da dattawa. Amma wasu mazauna Lagos da wasu yankuna na korafi kan rashin kai kayan zabe a kan kari.

https://p.dw.com/p/4NyTX
Masu kada kuri'a a Lagos bayan makara da aka yi wajen kai kayan zabeHoto: Christopher Onah/Focal Point Agency/IMAGO

Da yawa daga cikin 'yan Najeriya na fata zaben na wannan Asabar da ya hada da na wakilan majalisun dokoki, zai samar musu da sabon shugaba da zai sanya kasar mai yawan al'umma da kuma karfi tattalin arziki a Afirka kan sabuwar turba, bayan kwashe shekaru barkatai ana fama da tashe-tashen hankula da wahalhalu. Duk da cewa a wasu tashoshin zabe an bude rumfunan zabe a kan lokaci amma a da dama a fadin kasar an samu jinkirin isar jami'an zabe.

'Yan takara 18, maza 17 da mace daya ne ke takarar neman kujerar shugaban kasar, amma biyu ne daga cikinsu wato na manyan jam'iyyun da tun bayan komawa mulkin dimukuradiyya 1999 ke jan ragama, kuma dadaddun 'yan siyasa ake hasashe takarar za ta fi zafi. Sai kuma wani dan takara na wata karamar jam'iyya wanda kuri'a jin ra'ayin jama'a ta ce zai taka rawar gani musamman saboda goyon baya da yake samu daga matasa.

Za a fara kidayar kuri'u da zara an rufe rumfunan zabe a kuma lika sakamakon wucin gadi a wajen tashoshin zabe. Amma bayan kwanaki biyar ake sa ran samun sakamakon karshe daga jijoji 36 hade da babban birnin Abuja.