An tsawaita tsagaita wuta a Gaza da kwana guda
November 30, 2023Ministan harkokin wajen kasar Qatar Majed al-Ansari ne ya sanar da wannan labari a cikin wata sanarwa da ya fidda, inda ya ce an cimma wannan matsaya ne tare da tsoma bakin kasashen Amurka da kuma Masar.
Karin bayani: Gaza: Fatan tsagaita wuta na din-din-din
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin cikar wa'adin yarjejeniyar kwanaki shida da bangarorin da ke gwabza fada suka cimma wanda ya kawo karshe da asubahin ranar Alhamis (30.11.2023).
Karin bayani: Kokarin tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
Tuni ma dai kungiyar Hamas da kasashen Yamma ciki har da Amurka da Jamus suka ayyana a matsayin kungiyar 'yan ta'adda, ta tabbatar da wannan labari na tsawaita wa'adin yarjejeniyar wacce ke ke ba da damar isar da kayan agaji a zirin Gaza.
A daya gefe kuma sakataren Harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa Isra'ila inda yake ganawa da firaminista Benjamin Netanyahu kan rikicin da ya barke tun a ranar bakwai ga watan Oktoban da ya gabata.