Kokarin tsawaita tsagaita wuta a Gaza
November 29, 2023Yarjejeniyar tsagaita wutar kwanaki shidan dai ta fara aiki a ranar Jumma'ar makon da ya gabata dai, na da nufin samar da kafar shigar da kayan agajin jin kai zuwa yankin Zirin Gaza da yaki ya daidaita da kuma musayar fursunonin Falasdinu da ke jibge a kurkukun Isra'ila da kuma mutanen da kungiyar Hamas mai gwagwarmaya da makamai a yankin na Zirin Gaza ke garkuwa da su.
Karin Bayani: Hamas ta sako mutane 17 yayin yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila
Ya zuwa yanzu dai ana iya cewa kwalliya na biyan kudin sabulu, daga munanan hare-haren Isra'ila da Falasdinawan da ke zaune a Gaza suka fuskanta cikin makonnin da suka gabata ba tare da kakkautawa ba. Isra'ilan dai ta amince da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar a kan sharadin sakin mutane 10 a kowace rana, kuma Hamas ta amince da mika wasu daga cikin mutanen da take garkuwa da su kamar yadda ta yi tun daga ranar Jumma'ar. Ya zuwa yanzu dai an saki mutane 81 daga cikin sama da 200 da Hamas din ke garkuwa da su, yayin da aka saki Falasdinawa kusan 200.
To sai dai a yayin da kasashen duniya ke kokarin kawo karshen wannan rikici da ke zama mafi muni a shekarun baya-bayan nan, Isra'ila ta lashi takobin kawo karshen shekaru 16 na mulkin Hamas a Zirin Gaza kamar yadda Framinista Benjamin Netanyahu ke ci gaba da nanatawa. A daidai lokacin da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke taro na musamman domin lalubo hanyoyin warware rikicin na yankin Gabas ta Tsakiya, al'ummar Falasdinu musamman na yankin arewacin Zirin Gaza na fatan za su ci gaba da kasancewa cikin yanayin da suke a tsawon kwanakin tsagaita wutar duk da cewar mafi yawansu ba su da wani abun dogaro.
Karin Bayani: Tsagaita wuta na kwana hudu a Gaza
Wasu unguwannin Gazan dai babu komai fyace barakuzan gine-ginen da hare-haren bama-baman dakarun Isra'illa suka sauke har kasa, kana wasu sun zama kango. Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce, duniya na kallon al'ummar Gaza cikin wani babban bala'i na jin-kai. A kan haka ne ya jaddada bukatar fadada yarjejeniyar tsagaita wutar da ke shirin karewa, tare da shaidawa zauren Kwamitin Sulhu na majalisar cewa duk da kokarin cimma tsawaita tsagaita bude wutar abun da al'ummar Falasdinu ke bukata shi ne damar samar da kayan agajin jin-kai kawai.