An kalubalanci zaben shugabancin Najeriya a kotu
March 19, 2019Dan takara neman shugabancin Najeriya na jam'iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar ya tunkari kotun musamman da ke sauraren kararakin zaben shugaban kasar ne a shari'a da ke nuna alamun za'a dauki dogon olokaci ana tafaka turanci a kan wannan al'amari, domin kuwa ya samu manyan lauyoyi har guda ashirin tare da shaidu sama da 400 domin kalubalantar zaben da yake bukatar kotun ta ayyana cewa shi ne ya lashe shi, ko kuma ma dai ta ce a sake zaben.
Tuni dai jamiyyar APC da ke mulki ta mayar da martani a kan wannan shari'a da ke kalubalanatar nasara da suka samu. Ibrahim Masari sakatare ne a jam'iyyar ta APC.
A yayin da aka share fage na fara tafka muhawara da ma kawo shaidu a wannan shari'a da duka jamiyyun biyu ke ja sosai. Ga injinya Buba Galadima ya ce akwai fa abin da suka taka a shari'ar.
Shari'a ta kalubalantar zaben shugaban kasa a Najeriya dai babban al'amari ne da akan kwashe lokaci mai tsawo ana fafatawa tun daga kotun farko har zuwa ta koli. Amma ga 'yan jamiyyar APC da aka kai su kara na cewa ba su da fargaba, kamar yadda Hon Hadiza Bukar Abba Ibrahim da aka sake zabenta a matsayin ‘yar majalisar wakilai ta bayyana.
Za a sa ido a ga yadda za'a fafata a wannan shari'a da tuni jamiyyar PDP ta fara koken hukumar zabe ta hana mata ikon bincika takardun zaben shugaban kasar duk da kotu ta bada izinin yin hakan.