SiyasaIngila
Ana dab da kammala zaben Burtaniya mai cike da tarihi
July 4, 2024Talla
Nan gaba kadan a wannan yammaci ake kawo karshen zaben 'yan majalisun dokokin Burtaniya, zaben da ke cike da tarhi da kuma daukar hankali.
Karin bayani : Al'ummar Burtaniya na zaben 'yan majalisun dokoki
Ana kallon zaben a matsayin wanda ka iya bude sabon babin siyasa idan har jam'iyyar Labour ta samu galaba kan jam'iyyar Conservatives ta masu ra'ayin rikau, wacce ta shafe shekaru 14 tana jan zare a madafun iko.
Karin bayani : Dubban bakin haure sun shiga Burtaniya
Akalla masu zabe miliyan 46 ne ake sa ran za su kada kuri'a wannan Alhamis domin sabunta kujeru 650 na majalisar dokokin kasar wacce ke da hurumin zaben Firaminista.