1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Al'ummar Burtaniya na zaben 'yan majalisun dokoki

July 4, 2024

Al'ummar Burtaniya sun fara kada kuri'ar zaben 'yan majalisun dokoki, wanda ka iya bude sabon babin siyasa idan jam'iyyar Labour ta yi galaba a kan jam'iyyar masu ra'ayin rikau da ta shafe shekaru kusan 14 tana mulki.

https://p.dw.com/p/4hqVJ
Dan takarar jam'iyyar Labour Keir Starmer da firaministan Burtaniya Rishi Sunak
Dan takarar jam'iyyar Labour Keir Starmer da firaministan Burtaniya Rishi Sunak Hoto: Phil Noble/dpa/picture alliance

Akalla masu zabe miliyan 46 ne ake sa ran za su fita rufunan zabe daga karfe bakwai na safiyar Alhamis domin sabunta kujeru 650 na majalisar dokokin kasar wacce ke da hurumin zaben Firaminista.

Karin bayani: Dubban bakin haure sun shiga Burtaniya 

Batun ficewar Burtaniya daga Tarayyar Turai da annobar Covid-19 da tsadar rayuwa da kuma karancin likitoci da tarin matsolin na ficen bakin da kasar ta yi fama da su na daga cikin abubuwan da suka haifar da fatan neman sauyi domin kawo karshen mulkin jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta Conservative na kusan shekaru 14.

Hasashe dai na nunar da cewa firaminista mai ci Rishi Sunak na iya rasa kujerarsa bayan ya gaza gamsar da al'ummar kasar a tsawon watanni 20 da ya kwashe a kan wannan mukami. A cikin dare bayan rufe runfunan zabe ne ake sa ran samun sakamakon wannan zabe da ka iya bude sabon babi a tarihin siyasar Burtaniya.